Labarai

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce za ta raba gidan sauro mai dauke da magani guda Miliyan 4 da Dubu Dari 5 ga iyalai miliyan 1 da Dubu Dari 8 a fadin jihar.

Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna, Dakta Aishatu Abubakar-Sadiq, ce ta bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudana.

Aishatu Abubakar ta ce za a gudanar da rabon tun daga ranar 30 ga Yuni zuwa 3 ga Yuli, tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar da Shirin Kawar da Maleriya na Kasa, da Kungiyar Catholic Relief Services, da Kungiyar Society for Family Health, da Kuma kungiyar yaki da cutar Malaria mai suna Malaria Consortium.

Aisha ta ci gaba da cewa za a hada rabon gidan maganin sauro da Kuma kamfen na shirin bada maganin rigakafin maleriya na SPAQ ga yara Yan kasa da shekaru biyu zuwa uku.

Daga nan sai ta roki alummar jihar da su mara wa wannan shirin baya ta hanyar gabatar da yaransu domin samun rigakafin

A cewarta, yara miliyan biyu ‘yan kasa da shekaru biyar ne za su amfana da maganin rigakafin daga watan Yuni zuwa Satumba, bisa tsarin shirin kasa na kawar da cutar maleriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button