Ketare

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargaɗin cewa yawan masu kamuwa da cutar amai da gudawa wato kwalara a Sudan zai ƙaru, kuma akwai yiwuwar cutar ta yaɗu zuwa ƙasashen maƙwabta, ciki har da Chadi, inda dubban ‘yan gudun hijirar da yaƙin basasar Sudan ya raba da muhallansu ke zaune a wuraren da suka cika da mutane

SUDAN

Yaƙin da ya shafe fiye da shekaru biyu tsakanin sojojin Sudan — waɗanda suka karbe iko da Jihar Khartoum gaba ɗaya — da dakarun RSF ya haddasa yunwa da yaɗuwar cututtuka tare da lalata mafi yawan cibiyoyin kiwon lafiya.

Harin jiragen sama marasa matuƙa a makonnin da suka gabata ya katse wutar lantarki da ruwan sha a babban birnin Khartoum, wanda hakan ya ƙara yawan masu kamuwa da cutar a yankin.

Ya bayyana cewa cutar kwalara ta kai jihohi 13 a Sudan, ciki har da Arewaci da Kudancin Darfur waɗanda ke iyaka da Chadi, kuma mutane 1,854 sun riga sun mutu a wannan sabon yanayi yayin da damina mai haɗari ke ƙaratowa.

Ya yi kira da a samar da hanyoyin jin ƙai da kuma tsagaita wuta na wucin-gadi domin gudanar da kamfe na musamman domin allurar rigakafi kan cutar kwalara da sauran cututtuka kamar zazzaɓin Dengue da maleriya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button