Labarai
Hukumar Jin dadin Alhazai ta kasa NAHCON ta tabbatar da aniyarta na dawo da dukkan Alhazan Najeriya da ke Saudiyya zuwa ranar 28 ga watan Yunin, 2025.

Rahotanni daga Hukumar NAHCON da ke birnin Makkah na cewa, alhazan Najeriya 6,528 ne suka dawo Najeriya, yayin da Kamfanin Max Air ya kammala jigilar Alhazai jirgi na 16 a ranar Talata.
Wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan yaɗa labarai Fatima Sanda Usara ta fitar ta ce NAHCON tare da hukumar jin daɗin alhazai ta jihohi da kuma masu jigilar jiragen sama na shekarar 2025 suna yin duk abin da za su iya don ƙara saurin jigilar.




