Labarai
Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda aka dakatar daga wakiltar Kogi ta Tsakiya, a gaban kotu a Abuja bisa zargin yin ƙarya da ɓatanci.

An gurfanar da ita a gaban Mai Shari’a Chizoba Orji a Babban Kotun Babban Birnin Tarayya.
Gwamnatin ta shigar da ƙara kan tuhume-tuhume guda uku da suka shafi zargin ɓata sunan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.
An ce zargin ya samo asali ne daga wasu kalamai da ake zargin Sanata Natasha ta faɗa a bainar jama’a, inda ta yi iƙirarin cewa waɗannan manyan ’yan siyasa biyu sun haɗa baki don kashe ta.




