Matsalar yanayi tana haifar da tashin farashin abinci a duniya, in ji masana kimiyya

Binciken da aka saki a ranar Litinin ya bayyana wasu misalai da suka tabbatar karuwar kashi 280 cikin 100 na farashin koko a duniya a watan Afrilu 2024, bayan zafin rana a Ghana da Ivory Coast, da kuma karuwar kashi 300 cikin 100 na farashin letus a Ostiraliya bayan ambaliyar ruwa a 2022.
Kabejin da Koriya ta Kudu Ke Samarwa sannan da letas na Ostareliya, sai shinkafa ta Japan, da kofi na Brazil dakuma koko na Ghana suna daga cikin abinci da suka fuskanci tashin farashi bayan munanan yanayi tun daga shekarar 2022, wata tawagar masana kimiyya ta kasa da kasa ta gano.
A mafi yawan lokuta, karin farashin ya zo nan da nan bayan zazzafan zafi, ciki har da karin farashin kabeji da kashi 70 cikin dari a Koriya ta Kudu a watan Satumba 2024, karin farashin shinkafa da kashi 48 cikin dari a Japan a watan Satumba 2024, da karin farashin dankali da kashi 81 cikin dari a Indiya a farkon 2024.
Binciken, wanda aka buga ta kungiyoyin bincike guda shida na Turai tare da Babban Bankin Turai, an saki shi kafin Taron Tsarin Abinci na Majalisar Dinkin Duniya, wanda za a gudanar tare da hadin gwiwar Habasha da Italiya a Addis Ababa, Habasha, daga 27 ga Yuli zuwa 29 ga Yuli.




