Ketare

Ansamu Barkewar cutar amai da gudawa a babban birnin Sudan akalla mutane 70 suka Mutu a cikin kwanaki biyu yayin da ake ci gaba da yaƙi a ƙasar

Ma’aikatar lafiya ta Khartoum itace ta fitar da sabbin alkaluman waɗanda suka kamu da cutar har mutum 942 yayinda mutum 25 suka mutu a ranar Laraba, bayan samun mutane 1,177 da suka kamu da cutar da mutuwar mutane 45 a ranar Talata.

Kwamitin Ceto na Duniya (IRC) ya ce a cikin wata sanarwa yana “matukar damuwa da zullumin dawowar cutar amai da gudawa a Khartoum da fadin Sudan”, yayin da kasar ke ci gaba da fama da abin da tuni ya zama mummunan rikicin jin kai.

Karuwar yaduwar cutar amai da gudawa ta zo ne makonni bayan hare-haren jiragen sama marasa matuka da aka dora wa laifin rundunar sojojin sa kai ta Rapid Support Forces (RSF) suka katse ruwan sha da wutar lantarki a fadin babban birnin.

Gwamnatin da sojoji ke mara wa baya ta sanar a makon da ya gabata cewa ta kori mayakan RSF daga wuraren su na karshe a Khartoum watanni biyu bayan sake kwace tsakiyar babban birnin daga hannun ‘yan sandan soja.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button