Ketare
Yaƙin da ake tsakanin Iran da Isra’ila ya tayar da hankali a Pakistan yayin da ake fargabar kan tsaron kasarta

Pakistan na ci gaba da gudanar da harkokin diflomasiyya a tsaka mai wuya tsakanin Isra’ila da Iran, tare da fargabar ballewa da cigaba da Zaman ɗar ɗar.
A watan Janairu 2024, Pakistan da Iran sun harba makamai masu linzami zuwa cikin yankunan juna a cikin wani ɗan gajeren atisayen soji tsakanin makwabtan.
Duk da haka, bayan watanni 17, bayan Isra’ila ta kai hari kan Iran tare da kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran, kuma ta kashe janar-janar da masana kimiyyar nukiliyar Iran da dama, Pakistan ta yi saurin yin Allah wadai da matakin Isra’ila.
Islamabad ta bayyana hare-haren Isra’ila a matsayin take hakkin ikon mallakar ƙasa na Iran kuma ta kira su “tsokana bayyananniya”.




