Labarai
Shugaban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL, Bayo Ojulari, ya bayyana a wurin aikinsa da safiyar Litinin duk da rade-radin cewa ya yi murabus daga mukaminsa.

Ojulari, wanda ake zargin ya ajiye aiki a ƙarshen mako, ya isa ofishinsa da misalin ƙarfe 9:35 na safiya, lamarin da ya kawo ƙarshen ce-ce-ku-ce da ke yawo a kafafen sada zumunta.
Wata majiya daga sashen tsaro ta bayyana wa jaridar Vanguard cewa babu gaskiya a zancen murabus ɗin Ojulari, tana mai cewa tuni aka umarci ma’aikatan kamfanin da su yi watsi da duk wani labari da ke yawo game da hakan. Sai dai har zuwa yanzu, ba a bayyana inda Ojulari ya ke kafin dawowarsa ba, ko dalilin da yasa aka dade ba a ji duriyarsa ba.
Tuni Ojularin, bayan komawar ta sa office a litinin din nan, ya halarci taron da ƙungiyar injiniyoyin man fetur ta Najeriya ta shirya a jihar Legas ta manhajar Zoom.



