Ketare

Mutum 16 sun mutu a hare-haren Rasha mafi muni a Kyiv cikin kusan shekara guda

Rasha ta kaddamar da farmakin daruruwan jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami a kan birnin Kyiv daga daren Litinin zuwa Talata, inda ta kashe fiye da mutane goma sha biyu a daya daga cikin manyan hare-harenta a kan babban birnin Ukraine.

Hukumar Agajin Gaggawa ta Ukraine ta ce akalla mutane 16 sun mutu a Kyiv, kuma 134 sun jikkata.

Harin da Rasha ta kai ya kasance mafi muni a kan babban birnin cikin kusan shekara guda, in ji Hukumar Kula da Hakkin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya a Ukraine (HRMMU) a ranar Talata.

Ma’aikatar tsaron Ukraine ta ce ayyukan ceto na ci gaba da gudana har zuwa yammacin Talata, yayin da ake kyautata zaton akwai karin mutane a cikin baraguzan ginin da Rasha ta kaiwa hari

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button