Ketare
Mali ta fara gina masana’antar tace zinariya da Rasha ke mara wa baya

Sojojin mulkin ƙasar Mali sun fara gina wata masana’antar tace zinariya tare da hadin gwiwar wata babbar kungiyar Rasha, Yadran Group.
Shirin zai wakilci ikirarin ƙasar Afirka ta Yamma na “yancin tattalin arzikinta”, kuma zai tabbatar da cewa ƙasar ta amfana daga arzikin ma’adinanta, in ji shugaban soji Janar Assimi Goïta.
Hakan Ya karfafa dangantakar soja da tattalin arziki tare da Rasha tun bayan karɓar mulki a juyin mulki a shekarar 2021, yayin da yake rage dangantaka da tsohuwar ƙasar da tayi mulkin mallaka ga ƙasar wato Faransa da sauran ƙasashen Yamma.
Wannan yana nuna wata babbar alama a yankin, inda makwabtan ta Burkina Faso da Nijar suma suka karkata zuwa Rasha bayan kifar da shugabannin farar hula.




