Labarai
Yaƙin Iran Ya Lakume Wa Amurka Dala Biliyan 3.7 Cikin Sa’o’i 100 – CSIS

Binciken da Center for Strategic and International Studies (CSIS) da ke birnin Washington, D.C. ta gudanar ya kiyasta cewa Amurka ta kashe kimanin dala biliyan 3.7 a cikin sa’o’i 100 na farkon yaƙin
Rahoton ya nuna cewa tsadar yaƙin ta karu ne sakamakon amfani da manyan jiragen yaƙi, makamai masu linzami da sauran kayan yaƙi na zamani masu tsada da Amurka ke amfani da su wajen kai hare-hare.
A cewar cibiyar, yaƙin wanda ya shiga rana ta bakwai a ranar Juma’a, ya sanya Amurka kashe kuɗi fiye da yadda ake zato, yayin da kuɗin da Iran ke kashewa a yaƙin bai kai na Amurka ba sosai.
Masana sun yi gargadin cewa idan yaƙin ya ci gaba da ɗaukar lokaci, hakan na iya ƙara tsananta nauyin kuɗin da Washington ke kashewa a fagen yaƙi.




