Babban Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Mista Kayode Egbetokun, ya amince da ƙarin wa’adin jinkirta fara aiwatar da doka kan buƙatar samun izinin amfani da gilashin mota mai duhu (Tinted Glass Permit) zuwa ranar 12 ga watan Agusta.

Jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ‘Yan Sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Abuja.
Adejobi ya ce ƙarin wannan wa’adi ya biyo bayan damuwa da Kuma Jin ra’ayoyin da jama’a suka nuna dangane da farfado da tsarin yin rajista da samun izinin amfani da gilashin duhu ta hanyar intanet.
Ya ƙara da cewa ƙarin lokacin an yi shi ne domin ba da damar inganta tsarin, da kuma tabbatar da cewa ba a zalunci duk mai neman izinin ba.
A cewarsa, rundunar ‘Yan Sanda na ci gaba da aiki tukuru wajen sauƙaƙa tsarin neman izinin, ta hanyar hanyoyin kai-tsaye da kuma na nesa domin sauƙaƙawa alumma
Ya ce manufar ita ce inganta tsarin tantance sahihancin masu nema da kuma daidaita matakai domin rage jinkiri da kawar da matsalolin da ke dabaibaye fa shirin.




