Ketare
Iran ta yi gargadi cewa za ta kai hari kan sansanonin Birtaniya, Amurka da Faransa a yankin idan suka taimaka wajen kare Isra’ila

Iran ta yi gargaɗi ga Amurka, Birtaniya da Faransa kada su taimaka wa Isra’ila wajen dakatar da hare-haren ramuwar gayya na Tehran, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters yana ambaton kafafen yada labarai na gwamnati na Iran.
Rahotanni sun ce Tehran za ta kai hari kan sansanonin soja da jiragen ruwa da ke yankin idan kasashen uku suka ba da goyon baya ga Isra’ila.
Saidai Kuma ƙasar birtaniya tace babu wata bukata daga Isra’ila zuwa Birtaniya don irin wannan taimako.
Daga fadar Downing Street ba su mayar da martani ga waɗannan maganganun ba, amma tun daga safiyar yau an fahimci cewa Biritaniya ba ta shiga cikin wani aikin soja ba, ciki har da ƙoƙarin kare Isra’ila daga waɗannan hare-hare.




