Labarai
Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyar ɗaukar matakai masu tsauri kan duk wanda aka samu da hannu a harkar fasa bututun mai da satar ɗanyen mai a yankin Niger Delta.

Daraktan Tsaron Makamashi a Ofishin Mai baiwa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA), Hon. Ojukaye Flag-Amachree, ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da kamfanin Pipeline Infrastructure Nigeria Limited (PINL) ya shirya a birnin Fatakwal.
A cewarsa, tuni sama da mutum 100 da ake zargi da hannu a wannan haramtacciyar harka an gurfanar da su a gaban kotu.
Ya ce duk wanda aka kama, komai muƙaminsa, za a hukunta shi bisa doka.
Ya kuma roki shuga bannin al’umma da su ja kunnen matasa da yara kada su shiga lalata bututun mai.




