Masar ta kama masu rajin goyon bayan Falasdinawa kafin gangamin nuna goyon baya ga Gaza

Hukumomin Masar sun tsare fiye da masu rajin goyon bayan Falasdinawa 200 da suka iso birnin Alkahira ta jirgin sama a matsayin wani bangare na tattakin nuna goyon baya ga Gaza don matsa lamba kan kara samun damar agajin jin kai zuwa yankin. Wani ayarin motocin da ya bar Tunisiya zuwa Gaza a halin yanzu an tare shi a Libya.
Waɗanda aka tsare sun haɗa da mutane daga Aljeriya, Ostareliya, Faransa, Maroko, Netherlands, Spain da Amurka, in ji shi.
Fiye da masu rajin Faransa 20 da suka shirya shiga zanga-zangar [Jumma’a] an tsare su a filin jirgin saman Cairo na tsawon awanni 18, in ji shi.
Hukumomin Masar sun ce matakan sun biyo bayan gazawar bin hanyoyin da suka dace, ciki har da samun izini daga ofisoshin jakadanci da kuma samun biza.
Bayan watanni 21 na yaki, Isra’ila tana fuskantar karin matsin lamba daga kasashen duniya don ta ba da damar karin taimako ya shiga Gaza, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta kira “wurin da ya fi yunwa a duniya”.




