Ƴansandan Indiya Sun Kama Ƴan Najeriya 109 Bisa Zargin Zama Ba Bisa Ka’ida Ba

Rundunar ƴansandan jihar Maharashtra a ƙasar Indiya ta sanar da kama ƴan Najeriya 109 bisa zargin zama ba bisa ka’ida ba a ƙasar, tare da ƙwace hodar iblis a yayin wani samame da suka kai a yankin Nalasopara.
A cewar hukumomin tsaron, babu ko ɗaya daga cikin mutanen da aka kama da ke da cikakkun takardun zama, inda suka bayyana cewa mutanen na zaune ne a birnin Nalasopara da ke gabashin jihar Maharashtra.
Mataimakiyar Kwamishinan ƴansandan yankin, Poornima Chowgule-Shringi, ta ce an kai samamen ne da misalin ƙarfe 6 na safiya, inda jami’an tsaro suka samu nasarar cafke mutanen.
Ta bayyana cewa, “a lokacin samamen ne muka samu damar ƙwace hodar iblis mai nauyin giram biyu daga hannun wani mutum.”
Jami’ar ƴansandan ta ƙara da cewa an dade ana samun rahotannin shigar ƴan ƙasashen waje daga Najeriya, Uganda da Ghana da ke zaune a yankunan Nalasopara, Achole da Tulinj, kan zargin hannu a safarar miyagun ƙwayoyi.
Ƴansandan sun ce suna ci gaba da bincike domin gano hakikanin rawar da mutanen da aka kama ke takawa, tare da ɗaukar matakan doka da suka dace a kansu.




