Fake Alert: ‘Yan Sandan Kano Sun Cafke Masu Sayen Motar ₦75m

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kama mutane uku bisa zargin sayen mota kirar Mercedes Benz GLE, fara ƙalau, ta hanyar amfani da fake alert.
Kamen ya biyo bayan umarnin Babban Sufeton ‘Yan Sanda na Ƙasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, PhD, NPM, kan ƙarfafa aikin tsaro ta hanyar intelligence-led policing da kuma sintiri na awanni 24 a fadin ƙasa.
A cewar wata sanarwa da Rundunar ta fitar, Sashen Musamman na Shiga Tsakani (Special Intervention Squad – SIS) ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ya kama Ibrahim Tijjani, Jamilu Auwal da Mohammed Nura Dauda a ranar 28 ga Janairu, 2026, a unguwa Kabuga da ke Kano.
Sanarwar ta bayyana cewa mutanen sun sayi motar ne daga Gwarinpa, Abuja, kan kuɗi Naira miliyan 75 (₦75,000,000) ta hanyar amfani da fake alert da wani mutum mai suna Ibrahim Yahaya, wanda yanzu haka ya gudu.
An samu nasarar ƙwato motar, kuma an miƙa ta ga Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya (FCT Police Command) domin ci gaba da bincike.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin bisa jajircewa da ƙwarewa, tare da yin kira ga al’umma da su kasance masu lura, su kuma rika kai rahoton duk wani abu da suke zargi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa


