Ketare
Trump na so a kori waɗanda ba su da muhalli daga Washington

Donald Trump ya ce yana son a kori mutanen da basu da gida daga Washington da masu laifi a gidan yari.
A wani saƙo da ya wallafa ɗauke da hoton tantuna da kayan bola, Mista Trump ya rubuta cewa za a kwashe marasa muhalli su kasance sun yi nisa sosai da birnin ƙasar, wanda ya ce hakan zai tsaftace birnin da ƙara tsaro.
Kafar watsa labaran Amurka na cewa ana shirin tura dubban jami’an tsaron zuwa birnin, duk da cewa Magajin Birnin, Murial Bowser, ta ɗage kan cewa ba a wani fuskantar barazana ta.