Labarai

‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 17 Kan zargin Fashi, da ta’ammali da Miyagun Ƙwayoyi da Lalata Dukiya a Jigawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama mutane 17 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da fashi da makami, safarar miyagun ƙwayoyi da lalata kayan gwamnati, a jerin samamen da aka gudanar a sassan jihar.

 

 

Kakakin rundunar, DSP Shi’isu Adam, ya ce an kwato makamai, miyagun ƙwayoyi, kuɗi da kayayyakin sata a yayin samamen, wanda aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Dahiru Muhammad.

 

Daga cikin nasarorin, an kama wasu da kuɗi da wayoyi a Dutse, da masu fashi a Malam Madori, da kuma masu lalata transformer a Kirikasamma da Birniwa, yayin da wasu da ake zargi da satar dabbobi suka tsere.

 

Rundunar ta tabbatar da cewa ana ci gaba da farautar waɗanda suka tsere tare da bukatar jama’a su bai wa ‘yan sanda haɗin kai domin tabbatar da tsaro a jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button