Yan Sanda Sun Ce Ba Za Su Bayyana Bayanai Kan Hare-haren Amurka a Sokoto Ba

Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels, inda ya jaddada cewa batun ya shafi tsaro, don haka dole ne a yi taka-tsantsan wajen bayyana cikakkun bayanai.
“A matsayimmu na rundunar ’yan sanda, mun san wasu abubuwa game da hare-haren, amma ba za mu yi magana a kai ba,” in ji Hundeyin.
Ya kuma ƙara da cewa rundunar ta tura jami’an tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa domin tabbatar da tsaro, musamman bayan rahotannin da ke nuna cewa wasu fararen hula na iya samun rauni ko rasa rayukansu sakamakon hare-haren.
Rahotanni sun nuna cewa a ranar 25 ga Disamba, 2025, ne Amurka ta kai hare-hare kan ’yanbindiga a Jihar Sokoto.
Ma’aikatar Tsaron Amurka ta bayyana cewa hare-haren sun yi sanadin kashe “’yanbindiga masu alaƙa da ISIS da dama,” kuma an aiwatar da su ne bisa umarnin gwamnatin Najeriya.



