Ketare

Faransa ta karfafa tsaro a cibiyoyin Yahudawa na kasar

Faransa ta kara tsaurara matakan tsaro a cibiyoyin ibadar Yahudawa da wuraren da Isra’ila da Amurka ke da su a cikin kasar a wannan Asabar don ba su kariya, sakamakon barkewar rikicin Iran da Isra’ila.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Bruno Retailleau, ya ce daukar matakin a wuraren ibada da al’adu ya zama wajibi, kasancewar akwai yiwuwar samun harin ta’addanci a wuraren.

Kamfanin dillanci labarai na Faransa AFP ya rawaito cewar kasar ce babbar matattarar Yahudawa a Turai.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce harin da Iran ta kai mata cikin dare ya jikkata dakarunta 7, a tsakiyar birnin Tel Aviv, da ke zama shelkwatar sojojinta da kuma ma’aikatar tsaro.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button