Ketare
Farashin man fetur a kasuwannin duniya yayi tashin gauron zabi bayan da Isra’ila ta tabbatar da kai hari kan Iran, lamarin da ya haifar da ƙaruwar fargabar rikici mai tsanani a yankin Gabas ta Tsakiya.

Yan kasuwa da masu zuba jari na nuna damuwa cewa rikici tsakanin Iran da Isra’ila na iya kawo cikas ga fito da man fetur daga wannan yanki mai albarkatun makamashi.
Farashin man fetur na da tasiri kai-tsaye ga farashin komai, kama daga kayan abinci i zuwa kuɗin sufuri da sauransu.
Masu nazarin tattalin arziki sun shaida wa manema labarai cewa ‘yan kasuwa a kasuwar makamashi za su riƙa sanya ido don ganin ko Iran za ta mayar da martani a cikin kwanaki masu zuwa.




