Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da aikin share magudanan ruwa na shekara-shekara a titin Baban Gwari Rondabout, yankin da ake fama da ambaliyar ruwa a tsakiyar birnin.

Babban matakin shine don hana ambaliya maimaitawa da inganta lafiyar muhalli gabanin damina.
Bikin kaddamar da aikin da aka gudanar a ranar Juma’a, kwamishinan muhalli da sauyin yanayi, Dakta Dahiru Muhammed Hashim ne ya jagoranta, wanda ya bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na dakile illolin da ke tattare da toshe hanyoyin ruwa da zubar da shara ba bisa kaida ba a cikin biranen Kano.
Shataletalen Baban Gwari, inda taron ya gudana, an dade ana fama da ambaliyar ruwa, wanda hakan ke shafar lafiya, da kuma zirga-zirgar mazauna yankin.
Kwamishinan ya kuma jaddada bukatar ganin al’umma su shiga cikin yaki da ambaliyar ruwa a birane.
Ya kuma ba da tabbacin cewa ma’aikatar ta na aiki tare da al’umma ta hanyar da aka tsara wanda zai baiwa mazauna damar sanar da gwamnati bukatun magudanan ruwa na cikin unguwanni. Tuni dai aka fara share wasu magudanan ruwan a wasu unguwannin , tare da kwashe sharar nan da nan don gujewa toshewar magudanan.




