Jiragen saman Ukraine sun kai hari kan sansanonin sojin saman Rasha a wani farmakin da ba a taba gani ba

Jiragen saman Ukraine sun kai hari kan sansanonin sojin saman Rasha a wani farmakin da ba a taba gani ba
Jiragen sama marasa matuki na ƙasar Ukraine sun kai hari kan sansanonin jiragen saman Rasha a wani mafi muni da girman hari na rana guda tare da harba Bama bamai tun bayan fara yaki tsakanin kasashen.
Jami’an gwamnatin Rasha sun ce wasu sansanonin sojojin sama sun fuskanci hare-haren jiragen sama marasa matuka a wani babban farmakin da Ukraine ta kai gabanin tattaunawar zaman lafiya da za a fara a Istanbul ranar Litinin.
Ma’aikatar Tsaron Rasha ta ce Ukraine ta kaddamar da hare-haren jiragen sama marasa matuka da Wanda jiragen suka nufi filayen jiragen saman sojan Rasha a fadin yankuna biyar a ranar Lahadi, wanda ya haifar da tashin wuta a wasu jiragen saman.
A daren Lahadi, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya yabawa harin jirgin sama maras matuki na Ukraine da ya kira “mai matukar kyau,” yana cewa ya jawo asara mai yawa ga Moscow.



