Labarai

IPI na bukatar a bude tashar rediyo da aka rufe a Neja nan take

Cibiyar Ƙasa da Ƙasa ta Ƙungiyar ‘Yan Jarida (IPI) a Najeriya ta yi Allah wadai da dakatar da Badegi 90.1 FM, wata tashar rediyo mai zaman kanta da ke aiki a Minna, Jihar Neja.

Rufe gidan rediyon wanda Gwamna Umaru Bago ne ya bayar da umarnin saboda zargin yada abun da ke sukar gwamnatinsa.

Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban IPI Nigeria, Musikilu Mojeed, da Mai Ba da Shawara Kan Harkokin Shari’a, Tobi Soniyi, suka rattaba hannu a kai.

Rahotonna ya bayyana cewa a watan Janairu 2025, an tsare Yakubu Mustapha, ɗan jaridar Peoples Daily kuma Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida na Chapel na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), na tsawon kwanaki uku.

Ya yi kira da a gaggauta cire dakatarwar da aka yi wa Badegi FM ba tare da wani sharadi ba, yana gargadi cewa rashin bin wannan umarni cikin sa’o’i 48 zai sa a saka sunan gwamnan a cikin masu take hakkin ɗan adam

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button