Labarai

Ba’a taɓa yin wani kwamitin da ya yi aika-aika irin aika-aikar da kwamitin gona na bangaren Gwarfa ya aikata ba a qaramar hukumar Tudunwada.

Abinda yake faruwa a qaramar hukumar Tudunwada jahar Kano.

Muftahu Ahmad, Shugaban Qungiyar kare hakkin Dan Adam ta “Alhakku Human Rights & Social Justice Organisation” a qaramar hukumar Tudunwada, shine ya bayyana wannan a cikin tattaunawar shi da kafar watsa labarai ta “Ahrasjo news” a ranar Asabar 07-06-2025.

Muftahu Ahmad ya yi wadannan bayanai ne a daidai lokacin da koken al’ummar garin Tudunwada ya yi tsanani akan wani Kwamitin qasa wanda Shugabancin qaramar hukumar Tudunwada ya kafa, domin gudanarwa a ɓangaren abinda ya shafi harkar gona.

Muftahu Ahmad ya ce bayan an samar da wannan Kwamitin a qaramar hukumar Tudunwada sai shi Kwamitin ya tuttura wakilan shi izuwa sassa daban daban na qaramar hukumar Tudunwada ciki harda Gwarfa.

Inda Muftahu Ahmad yake cewa Gwarfa wani daji ne da ya zama mallakar gomnatin jahar Kano hadi da wani ɓangaren wanda Qaramar hukumar Tudunwada take ikirarin cewa nata ne, tare da cewa akwai wadanda suke iƙrarin sunada shaidar takardun mallaka na gonakan da suke nomawa a wannan daji na Gwarfa.

Wanda dama shi wannan dajin na Gwarfa an sarrafa shi izuwa gonakai domin al’umma ta amfana da shi, duba da yadda yake neman zama barazana ga al’ummar wannan yanki baki daya, a cewar Muftahu Ahmad.

Ya qara jaddada mana cewa shi wannan dajin ya zama mafaka ta masu satar mutane a lokutan baya, domin kuwa akwai wani mai unguwa da aka taba yin awon gaba da shi, kuma acikin wannan dajin aka ajiye shi har saida aka biya makudan kudade sannan Allah ya yi fitowar shi daga hannun masu satar mutanen.

Don haka tun zamanin gomnatocin baya aka fara yayyanka wa al’umma manoma wannan dajin, domin su noma shi a sami saukin barnar da take gudana a cikin wannan dajin, kuma gomnatin bayan ta basu takardun mallaka, kamar yadda Muftahu ya shaida mana.

Ya ci gaba da cewa manoma suna nomawa kuma suna zaune lafiya cikin aminci a wannan yanki tun bayan da aka mayar da wannan dajin izuwa gonakai.

Ya ce amma bayan zuwan Hajiya Sa’adatu a matsayin shugabar qaramar hukumar Tudunwada qarqashin Jam’iyyar NNPP sai ta nada kwamitin da zai bibiyi kadarorin gwamnati (Asset Recovery Committee) kuma ya dawowa da gomnatin kadarorin ta, qarqashin jagorancin Malam Ibrahim Sa’ad.

Bayan kwamitin ya gama bincike da tantance kadarorin gwamnatin ya miqa mata report, duba da yanayin report din sai gomnatin ta yi umarnin a dakatar da duk wani mai takardar mallakar gona a wannan dajin na Gwarfa.

Muftahu Ahmad ya ci gaba da cewa Bayan gomnatin ta dakatar da kowa ta hanyar rubuta takarda zuwa ga Hakimi akan ya sanar da al’umma masu gonaki a gwarfa gomnati ta dakatar da kowa a wannan yanki na Gwarfa,

Muftahu Ahmad ya ce bayan gomnatin ta ce ta dakatar da kowa, amma daga baya sai suka sami bayanin cewa gomnatin ta naɗa kwamitin gona (Farm Land Committee) a qaramar hukumar Tudunwada.

Don haka sai kwamitin ya tuttura wakilan shi zuwa sassa daban daban na qaramar hukumar Tudunwada ciki har da wannan yankin mai suna Gwarfa, wanda aka baiwa shugaban kwamitin a yankin Gwarfa shine Ahmad Ibrahim Dauriya a cewar Muftahu Ahmad.

Ya qara da cewa hakika al’ummar wannan yanki sun shiga cikin tsanani mai muni sosai da gaske, a sanadiyyar zuwan Dauriya a matsayin shugaban kwamitin gona.

Muftahu Ahmad yace akwai masu qorafi da yawan gaske  a ofishin mu na (Alhakku Human Rights & Social Justice Organisation) akan abinda Dauriya yake gudanar wa a wancan yanki na Gwarfa.

Ya ce daga cikin masu korafin akwai waɗanda suka shaida mana cewa suna noma gona tsawon shekaru, sai rana tsaka za ka ga Dauriya ya yo tattaki dauke da wani qaton abin awon gona yana auna gonar ka, idan ka tambaye shi ko miye yake faruwa? sai ya kada baki ya ce qaramar hukuma ta qwace ta ce mu raba ma wasu mutanen daban.

Muftahu ya ci gaba da cewa wasu masu korafin kuwa sunce Dauriya ne da kan shi ya same su kuma ya shaida musu cewa qaramar hukumar Tudunwada ce ta umarce shi da ya karbe ko wacce gona ya raba ta gida biyu, ya baiwa mai gona rabi, sannan qaramar hukuma ta dauki rabi, amma duk da haka suma wadannan mutanen sai dai su sha a ta-mama ba za su sami koda kuyya daya ba.

Ya qara da cewa Dauriya bai tsaya iya nan ba, a binciken da suka yi sun gano gonakai masu tarin yawa da Dauriya ya qwace ba tare da ya basu koda taku daya ba.

Muftahu Ahmad yace akwai Shugaban Qungiyar CAN na qaramar hukumar Tudunwada shima yana noma gonar shi cikin qoshin lafiya, amma sai ya wayi gari da ganin Dauriya ya dira gonar shi ya daka mata daduma, ya qwace ta, sannan ya mallaka wa mahaifiyar shi (Dauriya) wannan gona baki dayan ta.

Ya qara da cewa akwai gonar da ‘Alhaji Shafiu gigi’ wani dan kasuwa a Tudunwada yake nomawa, mai yawan ehka 147, itama Dauriya ya yi tsalle ya dira cikin wannan gonar inda ya rarraba ta ya ce ya baiwa wasu shafaffu da mai kason su na qaramar hukumar ta Tudunwada duk a cikin wannan gona ta Alhaji Shafiu gigi.

Muftahu Ahmad yace abin takaicin kuma shine, akwai mutanen da muka binciko kwatakwata ba’a taɓa gonar su ba, har umarni ake yi kada a taɓa ma wane tashi gonar, wanda muna dauke da lissafin su.

Amma gonar talaka da wanda bashi da galihu tuni Dauriya ya faffarke ta inji Muftahu.

Ya ce, idan har Dauriya ya rage maka wani ɗan kaso a cikin gonar ta ka, to zai gaya maka yanzu harajin ya yi tashin gwauron zabi, qaramar hukuma ta ce dole sai ka biya 37,000 duk ehka daya, idan kuma ba zaka iya biya ba to za’a baiwa wasu gonar.

Muftahu Ahmad yace abin takaicin idan aka ɗauki kudi 37,000 aka baiwa Dauriya to sai ya bada receipt na naira 15,000 kacal.

Ya qara da cewa Dauriya yana nan da wani asusun ajiya (Moniepoint account ) wanda yake bayar wa a danna masa kudade a cikin shi.

Muftahu ya ce akwai wani Alhaji Yahaya Mato shima haka ya maka wa Dauriya 370,000 na ehka goman da Dauriya ya barmasa a cikin ehka Arba’in, amma abin takaicin shine receipt din 150,000 Dauriya ya bashi.

Bayan koken yayi yawa, Sai muka kirawo Dauriya gaban Kwamitin Neman Mafita domin a samar da mafita akan korafe-korafen al’umma akan shi.

Ya ce Bayan Dauriya ya halarci wannan taron Dauriya ya shaida mana cewa wannan korafe-korafen duk haka suke, amma shima umarni aka bashi daga Qaramar hukuma, kuma hatta asusun ajiya nashi da yake bayar wa umarni aka bashi ya aikata hakan, sannan maganar takardar shaidar biyan kudi itama haka aka umarce shi daga sama ya rinqa bayarwa.

Muftahu ya ce, Dauriya ya shaida mana cewa idan akwai mai qorafi to ya je wajen qaramar hukuma ya yi qorafin shi, domin ni haka aka bani umarnin in yi aiki na.

Muftahu Ahmad ya ce abin mamakin kuma shine a wajen wannan zaman har akwai shugaban babban kwamitin gona na gaba-dayan qaramar hukumar Tudunwada mai suna alhaji Salisu wato mai gidan shi Dauriya din, wanda anan take ya miqe ya shaida mana cewa hakika bai ji dadin wannan abin da Dauriya ya aikata ba, kuma shima ya bada shawarar kada Dauriya ya sanya kudin haraji ya kai 30,000 amma Dauriya ya je ya sanya haraji har naira dubu 37,000 kuma yana basu takardar shaidar biyan kudi ta  naira 15000, ba mu ji dadin wannan abin da Dauriya ya aikata ba.

Saidai Muftahu Ya ce hakika mu al’ummar Tudunwada alkhairin Hajiya Sa’adatu muka sani bamu san shartinta ba, don haka akwai alamar tambaya cewa wai itace za ta sanya a yi wannan aika aikar.

Ya ce hakika ba za mu iya gani kuma mu qyale wasu mutane suna amfani da qarfin mulki ko kusanci suna aikata abinda ba daidai ba, za mu yi magana kuma za muyi kira har izuwa lokacin da kukan zai isa inda ake da bukatar ya je.

Ya qara da cewa muna kira ga shugabar qaramar hukuma da ta gaggauta daukar qwaqwqwaran mataki domin kare mutuncin ta, da mutuncin gomnatinta hadi da mutuncin kujerar ta, domin hakan zai zamo izina ga wasu.

Muftahu Ahmad ya ci gaba da cewa maganar wai gomnati ta qwace gonakai kuma daga baya ta rarraba ma wasu mutanen, ai wannan tsohon wayau ne wanda wasu marassa ilimi da lissafi suke amfani da shi, wanda kuma a halin yanzu kowa ya san shi.

Ya ce wayau ne na wasu masu mulki da suke amfani da mulki, su ke qwace hakkin wani da sunan gwamnati ta dakatar da ikon mallakar wani don ta mallakwa wanda take so wato shafaffe da mai.

Ya qara da cewa wannan ya saɓawa kundin gudanarwa na Land Use Act, kai-tsaye ya saɓawa qa’ida ta doka, don hakane ma muke tunanin Hajiya Sa’adatu tanada ilimin addini da na zamani ba zata aikata wannan zaluncin da kama karya ba.

Muftahu Ahmad ya qara yin kira na biyu cewa: ina mai qara kira ga Hajiya Sa’adatu shugabar qaramar hukumar Tudunwada da ta gaggauta daukar mataki akan Dauriya sannan ta damqa shi a hannun hukuma domin a yi bincike kan abubuwan da ya gudanar.

Sannan lallai a sanya Dauriya ya bayyana ina yake kai sauran kudi naira 22,000 a cikin dubu 37,000 duk ehka daya, idan an bashi kudin, cewar Muftahu Ahmad.

Ya ci gaba da cewa lallai ne shugabar qaramar hukuma ta yi umarni da a mayar wa Jama’a kudaden su wadanda Dauriya ya yi awon gaba da su.

Sannan ina mai roqo da kira ga Hajiya Sa’adatu Shugabar qaramar hukumar Tudunwada da kada ta yarda a ziga ta izuwa canza tsarin gudanarwar mulkin ta na farko, wato daidaita adalci a tsakanin al’umma, ɗan jam’iyyar ta da wanda ba ɗan jam’iyyar ta ba, domin alamu sun fara nuna mana haka a halin yanzu, cewar Muftahu Ahmad.

Ya ce muna qara kira a gare ta kada ta yarda wasu tsirarun mutane su lalata mata goben ta.

A qarshe dai muna rokon Allah ya bamu zaman lafiya da adalci a cikin al’umma baki daya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button