Ketare

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Australia, inda suka rufe babbar gadar Sydney Harbour ta ƙasar.

SYDNEY

Sun gudanar da zanga-zangar ne kwana ɗaya bayan kotun ƙolin ƙasar ta amince a gudanar da gangamin a ranar Lahadi, duk da mamakon ruwan sama da aka tashi da shi.

Sun ɗaga kwalaye da ke ɗauke da rubuce-rubuce, suna kira ga ƴansiyasa da su sa baki domin kawo ƙarshen yaƙi a Gaza.

Shugaban WikiLeaks, Julian Assange na cikin waɗanda suka shiga zanga-zangar, tare da ɗan majalisar ƙasar, Ed Husic.

A shekarar 2023 ne aka taɓa rufe gadar Sydney Harbour na ƙarshe, lokacin da kusan mutum 5,000 suka gudanar da zanga-zanga.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button