Sanata daga Borno ta Kudu, Ali Ndume ya nesanta kansa daga goyon bayan da wasu gwamnoni suka bai wa Shugaba Bola Tinubu domin sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu.

Sanatan, wanda ya shafe sama da shekaru 20 a Majalisar Dokoki ta Ƙasa, ya kasance bako a shirin siyasa na Channels Television na ranar Lahadi, mai suna Sunday Politics.
A cewarsa, tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya samu goyon bayan gwamnoni nc22 na jam’iyyarsa ta Peoples Democratic Party (PDP) a zaɓen 2015, duk da haka ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
A ranar 22 ga Mayu, 2025, gwamnoni 22 na APC sun amince da Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027.
Ndume, babban jigo a jam’iyyar APC, ya ce bai goyi bayan wannan matakin da gwamnoni suka ɗauka ba, duba da cewa “halin da ake ciki a ƙasar yanzu yana da matuƙar muni.”
Ya koka da tsananin halin ƙuncin tattalin arziki, tsadar rayuwa da kuma matsalolin tsaro da ke addabar sassa daban-daban na Najeriya. Ya ce: “’Yan Najeriya ba su ganin wata alama ta bege, suna shakku da wannan ‘Renewed Hope’ (Sabon Bege).”



