An Samu arangama a kan iyaka tsakanin sojojin Uganda da na Sudan ta Kudu inda akalla mutane hudu sun mutu

Aƙalla membobi huɗu na rundunar tsaron Sudan ta Kudu sun mutu a wani fada da sojojin Uganda a kusa da iyakar kasashen biyu, a cewar jami’an yankin, yayin da tashin hankali ke ƙaruwa kan rikicin iyaka da ba a warware ba.
Kakakin rundunar sojin Ugandan Manjo Janar Felix Kulayigye ya bayyana a ranar Laraba cewa, sojojin kasar Sudan ta Kudu guda uku ne aka kashe a ranar Litinin din da ta gabata, bayan da sojojin Uganda suka bindige wani sojan su bayan da aka kashe daya daga cikinsu.
Sai dai Wani Jackson Mule, wani jami’in yankin a jihar Central Equatoria ta Sudan ta Kudu, ya ce ya karbi gawarwakin sojoji biyar.
Uganda tana da tarihin shiga cikin harkokin Sudan ta Kudu kuma ta dade tana ba da goyon bayan soji ga Shugaba Salva Kiir, ciki har da tura rundunar sojoji na musamman tun watan Maris.
Kakakin rundunar sojin Sudan ta Kudu, Manjo Janar Lul Ruai Koang, ya ce a ranar Laraba shugabannin soji daga Sudan ta Kudu da Uganda sun amince da tsagaita wuta nan take domin ba da damar gudanar da bincike kan sabon rikicin kan iyaka.



