Trump zaiyi wuya a kula yarjejeniyar kasuwanci bayan Canada ta yi nuni da amincewa da Falasdinu

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai yi wuya a kulla yarjejeniyar kasuwanci da Kanada bayan ta sanar da cewa za ta goyi bayan samun ‘yancin kan Falasdinawa, bayan misalan da Birtaniya da Faransa suka bayar a yayin da ake kara yin Allah wadai da yaki da Isra’ila ke yi a Gaza a duniya.
Sakon Trump ya zo ne kwana guda bayan Carney ya sanar da cewa Canada tana shirin amincewa da Jamhuriyar Falasdinu a zaman taro na 80 na Majalisar Dinkin Duniya a watan Satumba idan an cika wasu sharudda, bayan sanarwar da Faransa da Birtaniya suka yi kwanan nan.
Canada da Amurka suna aiki kan tattaunawa kan yarjejeniyar ciniki kafin 1 ga Agusta, ranar da Trump ke barazanar kakaba harajin kashi 35 cikin 100 kan dukkan kayayyakin Kanada da ba su cikin yarjejeniyar ciniki ta Amurka-Mexico-Canada.
Firaministan ya ce tsananin wahalar da fararen hula ke fuskanta a Gaza ya bar “babu wani lokaci na jinkiri wajen daukar matakin kasa da kasa da aka tsara don tallafawa zaman lafiya”.




