Tsunami ta afkawa sassan Rasha, Japan, Amurka bayan girgizar ƙasa mai girma a Rasha

Guguwar tsunami ta afkawa sassan Rasha, Japan da Amurka bayan girgizar ƙasa mai ƙarfi a gabar tekun Rasha, tare da bayar da gargadi ga wasu ƙasashe da dama, ciki har da Philippines da Ecuador.
Ana sa ran za a samu igiyoyin ruwa masu haɗari a fadin Latin Amurka da kuma wasu tsibiran Asiya da na tekun Pasifik daga baya a ranar Laraba.
Bidiyoyin da aka wallafa a kafafen sada zumunta na Rasha sun nuna gine-gine a garin sun nutse cikin ruwa, yayin da hukumomi suka ayyana yanayin gaggawa a duk fadin Gundumar Kuril ta Arewa.
Magajin gundumar, Alexander Ovsyannikov, ya ce an samu isasshen lokaci don kwashe kowa daga tsibiran da abin ya shafa. “Dukkan mutanen suna cikin yankin tsaron tsunami,” in ji shi a wani taron gaggawa.
Cibiyoyin Gargadi na Tsunami dake Amurka sun ce igiyoyin ruwa masu tsawo har zuwa mita 3 (9.8ft) na iya kaiwa Ecuador da Rasha, yayin da igiyoyin ruwa na mita 1 zuwa 3 (3.3-9.8ft) za su iya yiwuwa a Hawaii, Chile, Peru, Costa Rica, Japan da wasu tsibirai na Pacific.




