Ketare

Bincike ya nuna cewa ISIL ka Iya zama barazana mai girma a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da Gabashin Afirka

Bincike ya nuna cewa ISIL ka Iya zama barazana mai girma a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da Gabashin Afirka

Da sanyin safiyar Lahadi, 27 ga watan Yuli, wasu mahara dauke da makamai sun kai hari a cocin Katolika da ke yankin Komanda na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo (DRC), inda kimanin mutane dari suka taru domin yin sintiri na dare.

An kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu a harin, wanda ya janyo fushi da tofin Allah tsine daga Majalisar Dinkin Duniya da fadar Vatican.

Mata da maza da akalla yara tara ne aka ruwaito na daga cikin wadanda harin cocin Saint Anuarite ya rutsa da su, a cewar jami’an Congo, yayin da aka yi garkuwa da wasu yara masu shekaru tsakanin 12 zuwa 14.

An kuma kai hari tare da kona gidaje da shaguna da ke kusa da cocin, inda hukumomi suka gano karin gawarwakin a wurin. Akalla mutane 43 ne aka kashe gaba daya

Kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) – wata kungiya ce dauke da makamai da ke aiki a yankunan kan iyaka da ke hade DRC da Uganda makwabciyarta, wadda kuma ta yi mubaya’a ga ISIL (ISIS) – tun daga lokacin ne ta dauki alhakin kai harin a wani sakon da ta wallafa a shafin Telegram.

Yana daya daga cikin hare-hare da dama na kwanan nan daga wata kungiya da masana ke cewa tana sake dawowa da karfi a wata kasa da tuni take cikin rauni saboda fada da makamai.

Hakan ya zo ba da jimawa ba bayan da gwamnatin DRC ta sanya hannu kan muhimman yarjejeniyoyin taswirar zaman lafiya tare da Rwanda da kuma kungiyar ‘yan tawaye ta M23 da ke ci gaba da samun ci gaba a gabashin kasar, wanda ya haifar da tambayoyi game da lokacin da kuma dalilin tashin hankalin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button