Ketare

Ruwan sama mai tsanani, zaizayar kasa sun tilasta kwashe mutane da yawa a arewacin China

Ruwan sama mai tsanani ya kashe akalla mutane 30 kuma ya tilasta hukumomi su kwashe dubban mutane bayan yankunan arewacin China sun fuskanci ruwan sama mai karfi wanda ya haifar da zaizayar kasa, a cewar kafafen yada labarai na gwamnati.

Hukumomin da Ke Kula da yanayi sun ba da gargadin guguwar ruwan sama mafi girma na biyu a Beijing babban birnin kasar, da ke makwabtaka da Hebei da Tianjin, da kuma wasu larduna 10 na arewaci, gabashi da kudancin kasar Sin, in ji kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Talata.

Fiye da mutane 80,000 ne aka kwashe a babban birnin kasar Sin kadai, kamar yadda kafar yada labarai ta Beijing Daily mallakar gwamnati ta bayyana a shafukan sada zumunta.

Adadin mutanen da suka mutu ya fi yawa a Miyun, wani yanki na karkara a arewa maso gabashin tsakiyar birnin, in ji rahoton.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga hukumomi a daren Litinin da su shirya don yanayi mafi muni kuma su gaggauta kwashe mazauna wuraren da ambaliyar ruwa ke barazana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button