Labarai
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani sabon shirin bayar da lamuni da ake yi wa laƙabi da Asusun Tallafawa Ma’aikatan Manyan Makarantu (TISSF) da tsabar kuɗi har naira miliyan 10.

Waɗanda za su gajiyar shirin sun haɗa da ma’aikatan jami’o’i da kwalejojin kimiyya da fasaha da kwalejojin ilimi da suke faɗin Nijeriya.
Daraktar Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ce ta bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja, inda ta ce shirin zai inganta walwala da ci bunƙasa fannin ilimi.
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya ce wannan tallafi wani ɓangare ne na kokarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na inganta harkar ilimi a ƙarƙashin shirin renewed hope




