Labarai
Mataimakin babban sakataren hukumar kula da jami’o’i ta kasa, Chris Maiyaki, a ranar Juma’a ya yi kira ga jami’o’i da gwamnati da su kara kaimi wajen saka hannun jari a fannin samar da fasahar zamani domin bunkasa koyar da fasahar a jami’oi.

Maiyaki ya ce, maimakon zama kawai wani tsari na bayar da shaida a takarda, koyon fasahar zamani mayar da ilimi zuwa wani tsani don karfafawa da kuma samar da ‘yan kasa masu ilimin zamani, masu iya aiki, da kuma iya shiga cikin cigaban al’umma.
Ya bayyana cewa Bude tsarin koyarwa daga nesa ta kwamfuta a kasar yana da matukar muhimmanci ga ci gaban Najeriya mai dorewa don haka akwai bukatar a ci gaba da sanya ilimin zamani ya zama ga kowa sannan kuma mai arha don tabbatar da cewa ba’a bar wani dan Najeriya a baya ba.
Mataimakin babban sakataren hukumar ta NUC ya yi wannan kiran ne a yayin jawabin da ya gabatar a wajen taron rantsar da dalibai karo na farko na cibiyar karatu daga nesa ta jami’ar Babcock dake Ilisan Remo.



