Labarai
Shugaban karamar hukumar Dala, Alhaji Surajo Ibrahim Imam, ya bayar da tallafin naira miliyan Daya ga matasan da suka samu horo akan shirin kare alumma na Neighborhood watch.

Alhaji Surajo Imam ya bayyana cewa matasan sun dawo ne bayan sun kammala horo da aka shafe makwanni ana yi musu.
Ya yi kira gare su da su kasance masu kishin jiharsu da ƙasarsu Najeriya
Ya bayyana cewa aikin da aka sa su gaba shine kare dukiyoyin al’umma tare da tabbatar da zaman lafiya, ganin yadda suka samu horo mai kyau da tarbiyya.
Shugaban ya ce ya ba su tallafin ne domin taimaka musu da wasu bukatunsu, tare da yi musu addu’a zama alheri a cikin al’umma.




