Amurka, Isra’ila sun yi Allah wadai da matakin Faransa na amincewa da ƙasar Falasdinu

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce Washington “ta ƙi ƙwarai” da shirin Shugaban Faransa Emmanuel Macron na amincewa da ƙasar Falasɗinu, yayin da gwamnatin Shugaba Donald Trump ta sanar da cewa ba za ta halarci taron Majalisar Dinkin Duniya mai zuwa ba wanda ke neman mafita ta ƙasa biyu ga Falasɗinawa.
Rubio ya yi suka ga “shawarar ta Macron a wani rubutu da ya wallafa a X a daren Alhamis, inda ya ce “yana taimakawa ne kawai ga yada labaran Hamas.
Tun da farko, Macron ya ce zai tabbatar da shawarar Faransa na amincewa da kasar Falasdinu a hukumance a taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a watan Satumba.
Aƙalla ƙasashe 142 daga cikin mambobi 193 na Majalisar Dinkin Duniya a halin yanzu suna amincewa ko suna shirin amincewa da wata ƙasa ta Falasɗinu. Amma wasu ƙasashe masu ƙarfi na Yamma – ciki har da Amurka, Biritaniya da Jamus – sun ƙi yin hakan.
Mambobin Tarayyar Turai na Norway, Ireland da Spain sun nuna a watan Mayu cewa sun fara aiwatar da tsari don amincewa da ƙasar Falasɗinu.
Saidai amincewar Macron za ta sa Faransa – daya daga cikin abokan Isra’ila mafi kusa kuma memba ta G7 – ta zama kasa mafi girma kuma mafi tasiri a Turai da za ta dauki wannan mataki.




