Ketare

Adadin wadanda suka mutu a rikicin Thailand da Cambodia ya karu zuwa 16 yayin da mutane 120,000 suka tsere daga yankin kan iyaka

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon arangama tsakanin sojojin Thailand da Cambodia ya karu zuwa 15 a Thailand da daya a Cambodia, a cewar hukumomi, yayin da fiye da mutane 120,000 da ke zaune a bangarorin biyu na iyakar da ke raba kasashen biyu suka tsere daga rikicin da ke ci gaba.

Fada mai tsanani ya ci gaba a rana ta biyu a ranar Juma’a yayin da kasashen biyu suka yi musayar harbe-harbe da manyan bindigogi da roka, wanda ya zama mafi muni a tsakanin makwabtan kasashen kudu maso gabashin Asiya fiye da shekaru goma.

Ma’aikatar Lafiya ta Jama’a ta Thailand ta ba da rahoton cewa a kalla fararen hula 14 da soja daya aka kashe a Thailand lokacin da fada ya barke a ranar Alhamis, kuma wani jami’in lardin na Oddar Meanchey a kan iyakar Cambodia ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an kashe mutum daya kuma wasu biyar sun jikkata a hare-haren Thailand.

Fiye da fararen hula 30 na Thailand da sojoji 15 sun ji rauni, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Thailand, yayin da kimanin mutane 100,672 daga jihohi hudu na Thailand da ke iyaka da Cambodia aka mayar da su wuraren mafaka, in ji Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Thailand kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

Ma’aikatar Al’adu da Fasaha ta Cambodia ta yi ikirarin cewa hare-haren Thailand sun haifar da “babban lalacewa” Preah Vihear, wani wurin Tarihin Duniya da UNESCO ta ware a cewar The Phnom Penh Post.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button