Labarai
Kotu ta yanke ma G. Fresh Hukuncin zaman gidan gyaran hali a jihar Kano.

Wata babbar kotun taraya a nan Kano ta yankewa Abubakar Ibrahim Wanda ake fi sani da G. Fresh hukuncin daurin wata biyar a gidan gyaran hali ko kuma biyan tarar Naira 200,000, bayan samunsa da laifin wulakanta takardun kudi na Naira.
An gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun mai lamba ɗaya, bisa zargin watsa takardun kuɗi yayin wata huldar nishadi a shagon Rahama Sa’idu da ke unguwar Tarauni.
Bayan karanta masa tuhumar, G. Fresh ya amsa laifinsa, inda kotun ta yanke hukunci nan take.



