Labarai

Wasu mazauna Ƙaramar Hukumar Gusau da ke Jihar Zamfara, sun yi zanga-zangar lumana tare da neman gwamnati ta ɗauki mataki kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a yankin.

Zanga-zangar dai an yi ta ne da misalin ƙarfe 12 na ranar Laraba.

Jama’a da dama sun halarci zanga-zangar; wasu a kan babura, wasu a cikin motoci, wasu kuma a ƙafa.

Ƙauyukan da abin ya fi shafa sun haɗa da Mada, Ruwan Bore, Fegin Baza, Bangi, Lilo, Wonaka, da Fegin Mahe.

Mazauna yankunan sun ce sama da mutane 100 ’yan bindiga suka kashe a baya-bayan nan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button