Ketare

Brazil ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta jagoranci kokarin samar da zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine

Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva a ranar Asabar ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta haɗa wata ƙungiya ta ƙasashen da za’a ɗora wa alhakin neman warware rikicin Rasha da Ukraine.

Lula ya nanata wannan maganar a wani taron manema labarai tare da Shugaban Faransa Emmanuel Macron a wannan makon, yayin wata ziyarar kasar.

Duk da cewa Macron da Lula sun yaba da karfin dangantaka tsakanin Faransa da Brazil,a taron manema labarai na ranar Alhamis ya nuna bambancin ra’ayoyi kan mamayar Rasha a Ukraine.

 

Macron ya jaddada cewa bai kamata a dauki Kyiv da Moscow a matsayin daidai ba, sabanin matsayin da Brazil ta bayyana na kasancewa maras tsaka-tsaki kan rikicin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button