Idan Gwamnatinku ba ta daina kisan kiyashi a Gaza ba, ku shirya karɓan ƴaƴanku a cikin akwatunan gawa — Inji Abu Ubaida

Mai magana da yawun sojojin Al-Qassam Abu Ubaida ya ce: Asarar da aka yi wa Yahudawan mamaya a Khan Younis da Jabalia a yau, wani ɓangare ne na jerin ayyuka na musamman, kuma misali ne na abinda ke jiran sojojin mamaya a duk wani wuri da suke.
Yahudawan Sahyoniya ba su da wani zaɓi face su tilasta wa shugabanninsu su dakatar da kisan kiyashin da suke yi a Gaza, ko kuma su shirya domin ci gaba da karbar ‘ya’yansu a cikin akwatunan gawa.
A jiya ne Dakarun Hamas suka yi kwanton ɓauna wa Sojojin Mamaya na Isra’ila a cikin wani gida, inda suka tayar da Bom alhalin sojojin suna cikin gidan, hakan ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutune 5, tare da jikkata uku kamar yadda kafar Current Report ta ruwaito.
Isra’ila ta na ci gaba da kai munanan hare-harenta a Gaza, kamar yadda yau ta kai hari kan wani tanti dake Khan Younis wanda ya yi sanadin asarar rayuka tare da raunana yara masu yawa.




