Labarai

Najeriya za ta ciyo bashin fiye da dala biliyan 21

Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu ta karɓo bashin ƙasashen waje da ya haura dala biliyan 21 domin aiwatarwa da cike giɓin kasafin kuɗin shekarar 2025 zuwa 2026.

Majalisar ta bayyana cewa za a yi amfani da bashin ne wajen aiwatar da muhimman ayyukan ci gaban ƙasa, musamman a fannonin ababen more rayuwa, da tsaro, da noma da kuma gina ɗan Adam.

Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan basussukan cikin gida da na waje, Sanata Aliyu Wamako ne ya gabatar da rahoton karbar bashin yayin zaman majalisar a ranar Talata.
Sanata Wamakko wanda yake wakiltar shiyyar Sakkwato ta Arewa a zauren majalisar, ya ce an jinkirta amincewar rahoton ne saboda hutu na majalisa da kuma jinkiri wajen samun takardun daga Ofishin Kula da Basussuka (DMO).

Shugaban kwamitin kasafi, Sanata Olamilekan Solomon, ya ce bayyana cewa sahale wa shugaban kasar karbo rancen yana kan tsarin da doka ta bayar da dama kuma tuni an riga an haɗa bashin cikin tsare-tsaren kasafin kuɗi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button