Ketare

WHO ta ce sojojin Isra’ila sun kutsa kai gidan ma’aikatanta da babban rumbun ajiyarta a Gaza

Dakarun Isra’ila sun kutsa kai cikin wasu cibiyoyin kungiyar Lafiya ta Duniya (WHO) yayin da suka ci gaba da farmaki a Zirin Gaza, in ji Darakta Janar Tedros Adhanom Ghebreyesus a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.

Hakan ya faru sau uku in ji Ghebreyesus.

Ya ce, “Sojojin Isra’ila sun shiga cikin harabar, inda suka tilasta wa mata da yara fita da ƙafa zuwa Al-Mawasi a cikin Wani irin yanayi mara daɗi”

Tedros ya ce babban rumbun ajiyar WHO, da ke Deir al-Balah, shima ya lalace.

“A matsayinta na hukumar dake jagorantar lafiya, lalata ayyukan WHO yana ƙara kassara dukkan ayyukan kiwon lafiya a Gaza,” in ji Tedros. “Tsagaita wuta ba wai kawai ya zama dole ba ne ya zama wajibi domin Kula da waɗanda suke cikin mawuyacin hali.”

WHO ta bayyana cewa za ta ci gaba da kasancewa a Deir al-Balah kuma za ta ci gaba da ayyukanta duk da hare-haren na sojojin Isreala.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button