Labarai

Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, kuma ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Barista Ibrahim Kashim, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.

A cikin wata wasiƙa da ya aike wa shugaban jam’iyyar a mazaɓarsa ta Majidadi, ranar 21 ga watan Yuli, 2025, Kashim ya bayyana cewa ya fice daga PDP, amma bai bayana dalilin ficewarsa ba.

Ya rubuta cewa: “Bayan yin la’akari da lamarin sosai, ina so na sanar da ku cewa daga yau, na fice daga jam’iyyar PDP. Zan ci gaba da neman hanyar da zan yi wa al’umma hidima da sadaukarwa, gaskiya, amana da kuma tsoron Allah (SWT).”

Kashim ya gode wa shugabannin jam’iyyar a mazaɓarsa bisa damar da suka ba shi na zama ɗan jam’iyyar, wacce ta ba shi damar tsayawa takarar gwamna a zaɓen 2023.

A shekarar 2023, kafin babban zaɓe, Kashim ya janye takararsa don bai wa Gwamna Bala Mohammed damar tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button