Uncategorized

Mataimakin shugaban kasar Indiya ya sauka daga mukaminsa

Firaministan Indiya Narendra Modi ya yi wa Jagdeep Dhankhar fatan samun lafiya a cikin wani Sako da ya saki a ranar Talata, bayan shawarar mataimakin shugaban kasa na yin murabus bisa “shawarar likita.”

A ranar Litinin, Mataimakin Shugaban ƙasar Dhankhar ya yi murabus daga mukaminsa, yana mai bayyana damuwa kan lafiyarsa.

“Shri Jagdeep Dhankhar Ji ya samu damammaki da yawa don yi wa ƙasarmu hidima a wurare daban-daban, ciki har da matsayin mataimakin shugaban kasar India,” Modi ya rubuta a shafin sada zumunta na X.

Dhankhar ya rike mukamin mataimakin shugaban kasar Indiya tun watan Agustan 2022.

Duk da yake wannan mukamin na tsawon shekaru biyar ne a al’ada, ɗan shekaru 74 ya ce lafiyarsa ta fi komai muhimmanci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button