Labarai
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a tsananta hukunci kan masu cin zarafin ’ya’ya mata, yana mai cewa babu wani musulmi nagari da zai yi wa matarsa dukan da har zai yi mata lahani.

A yayin da yake tunatar da malamai da limamai kan muhimmiyar gudunmawar da za su bayar a wannan fage domin yi wa tufkar hanci, Sarkin ya bayyana damuwa kan yadda matsalolin fyade da kuma samun magidantan da ke dukan matansu suka zama ruwan dare a Jihar Kano.
Sarki Sanusi na wannan furuci yayin da ya karbi bakuncin tawagar cibiyar bunkasa bincike (dRPC) da kuma cibiyar nazarin addinin musulunci ta Jami’ar Bayero da ke Kano (CCID) suka kai ziyara fadarsa.



