Labarai
Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance.

Naijaonpoint ta ruwaito cewa Eno ya sauya sheƙa ne a ranar Juma’a a wani biki da aka gudanar a Uyo, babban birnin jihar, inda shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Hope Uzodinma na Jihar Imo, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Lagos, da wasu gwamnonin APC da jiga-jigan jam’iyyar suka halarta.
Yayin jawabi a wajen taron, Gwamna Eno ya bayyana cewa bai shiga jam’iyyar APC daga rauni ba, sai dai daga matsayi na ƙarfi.
Ya kuma jaddada muhimmancin da ke akwai na daidaita Jihar Akwa Ibom da tsarin siyasa na matakin tarayya.


