Ketare

Ministar Kwadago da Jinkai ta kasar Cuba, Marta Feito Cabrera, ta sauka daga mukaminta bayan ta ce babu mabarata a kasar, sai dai masu karyar kasancewa mabarata.

Fadar Shugaban Kasar a ranar Laraba ta sanar da cewa Ministar ta amsa kuskurenta sannan ta mika takardar ajiye aiki kan abin da ta kira “nuna rashin tausayi da rashin kwarewa a kan batun da yake da tasiri a siyasance a kasar.

Labarin dai na zuwa ne kwana daya bayan Ministar ta yi kalaman a gaban ’yan kwamitin majalisar kasar a kan talauci a kasar wacce tsibiri ce.

Marta tace an ga mutane, wadanda a Zahiri mabarata ne, amma idan aka kalli hannunsu, da tufar da ke jikinsu, za ka ga sun yi bad-da-bami a matsayin mabarata, amma a zahiri ba mabarata ba ne.

Nan take kalaman nata dai suka karade gari, musamman a shafukan sada zumunta, inda aka rika kiraye-kirayen ta ajiye mukaminta.

Kasar Cuba dai na cikin mawuyacin halin matsin tattalin arziki a ’yan shekarun nan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button