Labarai
Shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya ce haɗakar ƴansiyasa a jam’iyyar ADC alheri ce ga siyasar Najeriya, wanda a cewarsa hakan zai taimaka waje hana ƙasar faɗawa cikin siyasar jam’iyyar ƙwaya ɗaya tal.

Gbajabiamila ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a jihar Legas a jiya Asabar a mazaɓarsa da ke Surulere.
Sai dai tsohon shugaban majalisar wakilan ƙasar ya bayyana shakkunsa kan haɗakar, inda ya ce ce ba ya tunanin za ta yi wani tasirin a-zo-a-gani.
A Najeriya dai fitatun ƴan jam’iyyun hamayya irin su Atiku Abubakar da Peter Obi da Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi da sauransu ne suka haɗu a jam’iyyar ADC domin fuskantar zaɓen 2027, inda suke fata za su kayar da Bola Tinubu.




